/

An bukaci Najeriya ta kai wa Amurka dauki kan rikicin zabe

Karatun minti 1

Wasu ‘yan Najeriya masu amfani da shafukan Twitter, sun yi kira ga gwamnatin kasar kan ta kai wa kasar Amurka dauki sakamakon barkewar rikicin zabe.

Ana zargin magoya bayan shugaba Donald Trump da tada hargitsi a zauren Majalissar Dokokin Amurka yayin da ake tattaunawa kan batun bai wa Joe Biden shaidar lashe zaben kasar da aka gudanar a shekarar 2020.

DABO FM ta bibiyi muhawarar da ya Najeriya suke tafkawa a Twitter.

Wani amfani da shafin Twitter, Bello Shagari, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kai wa Amurka dauki domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Ya ce; “Ina rokon gwamnatin Najeriya ta shiga tsakanin kan abin da yake faruwa a Amurka. Dimokradiyya tana cikin tsaka mai wuya.”

Duk da wasu suna ganin mai rubutun yana zolayar ‘yan Najeriya ne da suke kai kukansu ga Amurka idan ana rikicin zabe a Najeriya.

Tin kafin sanar da Joe Biden a matsayin zababben shugaban Amurka, shugaba Donald Trump ya ce an tafka magudi a yayin zaben.

Lamarin da ya ce bai amince da sakamakon zaben ba, ya shiga kotuna da yawa domin kai kara, sai dai kotunan sun watsar da kararrakin sakamakon rashin hujjoji.

Shi ma a nasa bangaren, babban lauyan gwamnati ya ce babu hujjar da Trump yake da ita domin tabbatar da korafinsa.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog