Home LabaraiKotu koli ta haramtawa Gwamnoni nadin shugaban riko ko rushen shugabancin karamar hukuma

Kotu koli ta haramtawa Gwamnoni nadin shugaban riko ko rushen shugabancin karamar hukuma

by Dabo Online
0 comments

Babbar kotun Najeriya ta haramtawa Gwamnonin jihohi nadin shuwagabannin riko a kananan hukumomin jiharsu. Haka zalika ta haramtawa gwamnoni ikon cire rushen shugabancin karamar hukuma.

Hukuncin kotu da alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a OluboladeJoe suka zartar a ranar 11 ga watan Disambar 2019, sun soke dokar da ta bawa Majalissar Dokokin jihar damar tsige zababben shugaban karamar hukuma.

DABO FM ta tattaro cewa gamayyar alkalan sun tabbatar da cewar majalissar karamar hukuma ce kadai doka ta bawa damar tsige shugaban karamar hukumar da aka same shi da laifin da doka ta tanada.

Kotun tayi hukuncin ne biyo bayan daukaka kara da shuwagabannin kananan hukumomi 16 na jihar Ekiti suka daukaka kara gaban kotun koli bayan da sabon gwamnan jihar, Kayode Fayemi , ya tsige su, kamar yacce Daily Trust ta tabbatar.

Ana haka ne bayan hukuncin Kotun, Kansilolin a jihar Kaduna, a ranar 2 ga watan Janairun 2020, suka tsige shugaban karamar hukumar Zariya bisa kamashi da laifin mulkin kama karya.

Karanta cikakken bayanin anan: https://dabofm.com/kansiloli-11-cikin-13-sun-amince-da-tsige-shugaban-karamar-hukumar-zariya/

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00