Home LabaraiKotu ta soke zaben dan Majalissar APC a jihar Kano

Kotu ta soke zaben dan Majalissar APC a jihar Kano

by Dabo Online
0 comments

Kotun sauraron korafe korafen zaben Majalissar dokokin Najeriya dake da zama a jihar Kano, ta soke zaben da dan Majalissar tarayya na APC ya lashe.

Hukumar INEC dai ta ayyana Wanarabul Munir Dan Agundi a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a watan Fabarairun 2019.

Sai dai dan takarar PDP, Umar Ballah ne ya kai karar bisa rashin amincewa da lashe zaben da dan majalissar APC yayi.

Kotun ta jingine zaben tare da umartar sake zabe a mazabar Mariri.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00