Labarai Siyasa

Kotun sauraren zaben jihar Kano tayi barazanar mayar da zamanta zuwa Abuja

Kotun dake sauraren karar zaben gwamnan jihar Kano, tayi barazanar mayar da cigaba da Shari’ar zuwa babban birnin tarayyar Abuja.

Kotu ta bayar da kashedin ne a zamanta na ranar Labara bayan da lauyan hukumar INEC, Mista Adedeji, ya gabatar mata da korafin ci wa shaidar hukumar INEC mutunci.

DABO FM ta tattaro cewa; Lauyan INEC ya bayyana cewa anyi wa ma’aikaciyar INEC, Halima Sabo cin mutunci ne bayan da ta bada shaida akan zabe na biyu na gwamnan jihar Kano da aka gudanar a watan Maris.

Da take bayar da kashedin, mai Shari’a, Halima S Muhammad, tace bazasu lamunci barazana daga wajen ko waye ba akan membobin Kotu, kama daga basu bada shaida har ma’aikata.

Ta bayyana cewa; “Itace da kashin kanta tace ayi zaman kotun a jihar Kano domin baiwa al’ummar jihar damar gani da kuma jin abinda ke wakana akan shari’ar.”

“Amma idan hakan ya cigaba da faruwa, zan mayar da Shari’ar zuwa babban birnin tarayyar Abuja.”

Shima a nasu bangaren, lauyan daga cikin lauyoyin PDP, Barista Maliki Kulliya, ya ce wannan ba lamarin da za’a goyawa baya bane, domin hakan ya sabawa doka.

Karin Labarai

UA-131299779-2