Labarai

Manhajar Twitter ta samu tasgado

Shafin Twitter ya samu tasgado a yammacin ranar Laraba.

DABO FM ta bincike cewa shafin Twitter ya tsaya da aiki ne daidai misalin karfe 7:37 a agogon Kasar Indiya, karfe 3:07 agogon Najeriya da Nijar.

Makalewar Twittar ya haifar da rashin iya martani ko son hoto tare da rubutun da wani ya wallafa (Wanda ya rika ya bude tin kafin daukewarta).

Har zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, karfe 8:15 agogon Indiya, 3:45 na Yamma agogon Najeriya da Nijar, shafin Twitar bai cigaba da aiki kamar yacce aka saba ba.

Ba wannan ne karo na farko da kafafen sadarwar suke samu tangarda ba.

Idan ba’a manta ba, a kwana-kwannan nan ma manhajar Whatsapp ta samu tangarda, inda ya kasance masu amfani da manhajar basa iya bude hoto ko turawa, tangardar da ta shafe sama da sa’o’i kafin daga bisani manhajar ta cigaba da aiki.

Karin Labarai

UA-131299779-2