Bincike Labarai

Kudin yi wa Majalissa kwaskwarima zai ishi gina ajujuwan zamani guda 10,360

Kudade da aka ware na Naira biliya 37 domin gyaran Majalissar Najeriya wanda ya janyo cece-kuce tsakanin al’umma kasar musamman masana da suke ganin an saka koko ba’a masakinshi ba.

Al’umma suna gani a kasar da ake da matsalar Ilimi tare da kunci na talaucin da babu ranar fita, bai kamata ayi maganar gyaran Majalissar bama balle ware mata makudan kudaden da zasu taimakawa talakawa.

A wani bincike da DABO FM ta gudanar, bisa ga kiyasin samun ginannun ajujuwa a Naira miliyan 3 da rabi, Najeriya zata samu ajujuwa wanda adadinsu ya kai guda 10,360.

Hakan tare da ingantashi da zuba musu dukkanin kayyayakin karatu wanda suka kunshi, kujerun da teburan zamani na zama ga dalibai 50, teburin zaman malami, Allon bango guda biyu (Mai amfani da allin ‘Marker’ da Majigi) tare da Kwamfutar zamani a kowanne aji.

Tini dai gwamnati ta amince da kashe kudin bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin na shekarar 2020 wanda ya kama Tiriliyan 10.594.

Karin Labarai

UA-131299779-2