Labarai

Kungiyar ASUU ta tsage gida 2

ASUU

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU, ta rabu gida biyu bayan ficewar wasu ‘ya’yan kungiyar daga jikinta.

Tini dai daga cikin ‘yan kungiyar da suka balle suka ja layi tare da nadawa sabuwar kungiyarsu sunan ‘Congress of University Academics (CONUA).

‘Ya ‘yan kungiyar da suka kafa sabuwar kungiyar sun bayyana ficewarsu daga ASUU a matsayin wani yunkuri na dawo da martabar, inganci da kuma tsayuwar Ilimi a Najeriya.