0
Gidan Talabijin na Arewa 24 ya fitar da cigaban shirin Kwana Casa’in a manhajar Instagram.
Hakan na zuwa ne bayan cika alkawari da tashar tayiwa masu kallonta da cewa zasu cigaba da kawo sabon shirin a satin farko na watan Oktobar 2019.
Dabo FM ta bincika cewa yanzu haka Kwana Casa’in Zango na 2, kashi na 1, yana nan a kan tashar Youtube ta Arewa 24.
