Mintuna 149,760 tin bayan dauke Dadiyata

Matashi Abubakar Idris, wanda aka fi sani Abu Dadiyata, ya cika kwanaki 104 tin bayan da wasu ba’a san ko suwaye ba suka daukeshi har cikin gidanshi dake Kaduna.

Dadiyata ya shafe mintuna 149,760 wanda yayi dai dai da kwanaki 104 da daukewa.

Tin dai ranar 1 ga watan Agustar 2019, aka dauke matashin bayan shigar shi gidanshi, kamar yacce uwargidanshi ta tabbatar.

Dadiyata wanda ya kasance Malami a wata makarantar gaba da Sakandire dake jihar Katsina kuma jigo mai tashe a matasan shafin sada zumunta na na manhajar Twitter.

Dadiyata, yana daga cikin Matasa ‘yan gwagwarmaya masu wajen fafutikar kare darikar Kwankwasiyya a siyasance.

Masu Alaƙa  #PrayforDadiyata: Kwanaki 10 da bacewar Abu Hanifa Dadiyata 'Kwankwasiyya'

Har yanzu dai babu masaniya game da wadanda suka dauke shi ko sace shi, sai dai ana alakanta batan nashi da lamarin Siyasa.

Tin dai a watan Agusta, hukumar DSS ta tabbatar da rashin hannunta game da batan Dadiyata.

Sai dai a kwanakin da suka gabata, Alhaji Buba Galadima, ya zargi wasu gwamnoni da hannu wajen dauke matashin.

Kungiyoyin fafutukar kare hakkin bil adama na kasa Najeriya da kasashen waje, sun shiga sahu wajen yin zanga-zanga domin ganin an fito da Matashin daga inda aka ajiyeshi.

Akwai abubuwan tambaya da yawa wajen bacewar matashin, shin yana raye? Idan yana raye yana hannun wa? Yaya iyalinsa suke ciki? Me hukumomi suke a nemo inda yake? Me yan siyasa suka yi don ganin an nemo shi???

Masu Alaƙa  Kwankwaso ya roki jami'an tsaro na farin kaya su nemo inda Dadiyata yake

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na Facebook, Dabo FM.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.