Home LabaraiMAAN ta kaddamar da bai wa manoman jihar Kaduna tallafin aikin gona

MAAN ta kaddamar da bai wa manoman jihar Kaduna tallafin aikin gona

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

A kokarin ta na kyautatawa manoma masara domin wadata kasa da abinci, Kungiyar manoma Masara ta kasa, wato Maize Association of Nigeria (MAAN) da hadin gwiwan babban bankin Najeriya wato CBN karkashin shirin gwamantin tarayya na tallafawa manoma da rance mai taken Anco Borrowers, sun shirya tallafawa manoma shinkafa sama da dubi 90 a sassan kasar nan.

Da yake kaddamar da shirin ga manoman Jihar Kaduna, Shugaban Kungiyar manoma masara ta kasa Dr Bello Abubakar Annoor, ya ce a bana babban abin godiyar su ga Allah shi ne yadda aka bayar da kayan aikin Noman akan lokaci, sabanin yadda a shekarun baya akan ce an baiwa manoman kaya a kurarren lokacin, da hakan ta kan sa wasu ma su aje kayan da aka basu sai zuwa wani lokaci su yi amfani da shi.
A saboda haka duk manomin da yake manomi ne na gaskiya, ya kamata ya yi amfani da kayan da zai samu domin habaka aikin Noma a daminan bana.

Ya shawarci manoman su yi gaggawan komawa gona domin fuskantar aikin Gona saboda su biya abun da aka bashi cikin lokaci.

Ya kara da cewa, amfanin noma Masara a irin wannan lokaci ba Wai ya tsaya ne kadai ga manomin da zai noma domin cimaka ba, har ma da ciyar da kasa da abinci.

Dr Bello Annoor, ya bayyana babban kalubale da suke fuskanta a kowanni shekara shi ne rashin biyan bashin da wasu manoma suke yi da zaran sun samu amfanin gona, Kuma bayyana cewar hakan ba karamin cikas yake haifarwa ba wurin tallafawa sauran manoma masu tasowa.

Tunda farko shi Irin noma da taki har ma da sauran magungunan Noma an bada shi ne domin tallafawa manoma musamman a yankunan karkara, to amma abun takaici shi ne yadda wasu kan bijirewa biyan sakamakon abun da ake bukata daga gare su akan lokaci da zaran sun kammala aikin Gona.

Bisa wannan ne ma,ya ce sun samar da kwamitoci masu wayar da kan manoma akan muhinmancin biyan bashi, wanda suke fatan nan bada jimawa ba manomi zai biya bashi ba tare da an tunatar da shi ba.

A jawaban su daban-daban, wakilin babban bankin Najeriya CBN da na bankin Unity da shuwagabannin kungiyoyin Tumatir da Gyada ta Jihar Kaduna, sun jinjinawa Shirin na Kungiyar manoma masara ta kasa ne, tare da kokarin shugaba Muhammadu Buhari a kokarin su na tallafawa manoma a kasa baki daya, wanda suka kwatanta hakan da wani tsari da zai daura kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.

Sun kuma ja kunnen manona wurin maido da bashin da aka basu akan lokaci, domin an yi hakan ne da nufin tallafawa manoma masu dumbin yawa a tarayyar Najeriya.

Tun farko da yake jawabin maraba, Sakataren kungiyar manoma na Jihar Kaduna Alhaji Adamu Jibrin, ya tabbatar wa manoma cewa zuwa yanzu kaya na kasa kuma za’a baiwa manoma da wuri, kuma bisa yanda aka tsara bada tallafin zai kasance ne da zaran manomi ya cika duk sharuddan da ake bukata.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00