RAJASTHAN: Wata mata a jihar Bayelsa ta kwararawa mijinta tafasashen ruwan zafi bayan sun matsala tsakaninsu.
Rahotanni daga The Guardian sun ce matar da yanzu haka ta tsere, ta kwararawa mijin nata mai suna Misata Oyinkoro Miebode sa’ilin da yake kwance a dakin hutawa a gidansu dake unguwar Kpansia dake garin Yenagoa.
Da yake magana da jaridar ta The Guardian, Mista Oyinkoro ya bayyana cewa matar ta kwarara masa ruwan ne a ranar 3 ga Yuni, lamarin da ya sanya fatarshi ta daddaye sosai.
Mista Oyinkoro rikicinsu ya samo asali ne bayan da ya gaggauramata mari guda sakamakon zaginshi da tayi bisa dalilin zuwanshi da wuri wajen daukota daga wajen aiki saboda tace masa zatayi dare.
A cewarshi ya je wajen da sukayi zasu hadu da wuri ne sakamakon matsalar fashi da makami a yankin.
Ya yi bayanin cewa, matar tashi ta kirashi daga ofishinta don ya zo dauko ta a wani waje da misalin karfe 8 saboda za ta kai dare a wajen aiki. Oyinkoro ya ce ya tashi daga aiki da misalin karfe 6 na yamma, mai gidanshi ya kaishi dai dai wajen da suka yi da matar tashi za su hadu, ya kuma zauna yana jiran karfe 8 tayi.
Ya ce yana zazzgawa ne sai ya hangi matar tashi wajejn karfe 7 na yamma, ya ruga domin ya sanar mata cewar yazo, sai dai lamarin bai yi mata dadi ba domin ta ji haushi ya zo kafin lokacin da suka yi da shi.
Ya ce; “Cike da mamaki, na tambayeta meyasa take fushi domin nazo da wuri, kuma meyasa ba ta cemin inzo wajen da wuri ba nima. Daga nan ne ta fara zargin cewar ina saka mata ido. Ta fara zagi na har muka isa gida. Na zata zamu sasanta kanmu a gida amma abin yaci tura.”
“A cikin fushi, na mare ta sau biyu, na kuma umarce ta da ta shiga daki tayi bacci. Daga nan ne wani abikina ya kirani domin halartar taron murnar zagayowar haihuwarshi, ban dawo ba sai wajejen karfe 1 na dare.”
“Ina bacci a kan doguwar kujera a cikin falo, sai naji saukar ruwan zafi a jiki na.”
An yi ta kokarin samun matar domin amsa tambayoyi amma hakar ta gaza cimma ruwa.
