//

Ko shugaban karamar hukuma na samu, zan yi -Isa Yuguda

Karatun minti 1

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda yace a shirye yake da zama shugaban karamar hukuma idan mutane suka bukace shi da yin hakan.

Tsohon gwamna ya bayyana haka ne a labarar data wuce a gaban kwamitin tabbatar da kara zaben shugaba Muhammadu Buhari karo na biyu wanda mai gudanarwa a kwamitin, Sanata Godswill Akpabio ya jagoranta.

Isa Yuguda ya dauki matakin ne a shirin da yake na bada duk wata gudunmawa, duk kankantarta domin ganin an sake zaben shugaba Muhammad Buhari karo na biyu a matsayin shugaban Najeriya.

“Duk irin mukaman dana rike, gwamna wa’adin biyu, ministan har sau biyu, shugaban manyan bankuna biyu, a shirye nake da rike shugaban karamar hukumar domin taimakawa wannan tafiyar har a samu nasara.”

“Ya kamata mu girmama kawunan mu ba mukamanmu ba, dole sai mun zama tsintsiya madaurinki daya, ta hakane kawai zamu kai ga ci.”

Taron ya samu halartar daraktan yada labaran kwamitin, Dr Kelani Mohammed , tsohuwar shugaban mata ta jam’iyyar APC, Haj Ramatu Tijjani Aliyu , da sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog