Labarai

Mai cutar Kwabid-19 ta haihu a Legas, 3 sun mace, an sallami 67

An kara samun mai dauke da cutar Kabid-19 ta haife jariri a jihar Legas.

Majiyar Dabo FM ta bayyana gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwa-Olu ne ya sanar da hakan a kan shafinsa na Twitter.

Wannan na zuwa ne bayan kwana hudu da haihuwar wata mata mai cutar a asibitin Koyarwa na Idi-Araba.

Sai kuma rahoton da ya ishemu na mutum 3 sun rasu a jihar, rahoton da aka fitar ranar Juma’a, wanda ya hada jimillar mutane 36 ne suka rasa rayukan su.

Inda aka sallami mutum 67 kamar yadda rahoton Radio Nigeria ta bayyana a yammacin yau.

Karin Labarai

UA-131299779-2