Labarai

Majalissar Dattijai taki amince wa da kudirin hana shigowa da Injinan ‘Generator’

Majalissar Dattajai ta ki aminta da kudirin kakaba takunkumin domin hana shigowa da injinan ‘Generator’ cikin Najeriya.

Yayin zaman majalissar na ranar Talata, Sanata Chukwuka Utazi, mai wakiltar Enugu ta Arewa, ya kawo kudirin da zai shawo kan matsalar wutar Lantarki da ta dade tana ciwo kasar Tuwo a kwarya.

Sanatan dai yayi kira da Majalissar da ta binciki harkokin wutar Lantarki a kasar.

Haka zalika, Sanata Francis Fadahunsi, mai wakiltar Osun ta Gabas, ya bada shawarar kakaba hana shigowa da Injinan ‘Generator’ na tsawon shekara 5 cikin kasar, ko hakan zai taimaka wajen kawo karshen kalubalen wutar lantarkin.

Sai dai a lokacin da shugaban Majalissar, Ahmad Lawan, yayi kuri’ar jin ta bakin Sanatocin, sun ki amincewa da shawarar Sanata Francis akan hana shigowa da Injinan.

A nashi bangaren, Sanata Gershon Bassey, mai wakiltar Cross River ta Kudu, ya bayyana cewa akwai bukatar a samar da na’urorin rarraba wutar masu ingancin domin shawo kan matsalar rashin wutar a kasar.

Ya kara da cewa karfin na’urorin da ake dasu a kasar, bazasu iya daukar adadin wutar Lantarkin da zata wadata kasar ba.

Daga karshe ya shawarci gwamnatin tarayya ta dora akan tsaruka masu kyau na gwamnatin da ta shude.

Tini dai majalissar tayi kira ga gwamnati tarayya da ta inganta na’urorin samar da wutar Lantarki a kasar baki daya.

Haka kuma Majalissar ta baiwa Kwamitin wutar Lantarki na majalissar Dattajan makonni 4 domin yin bincike akan sha’anin wutar kasar.

Karin Labarai

UA-131299779-2