//

Babbar Kotu a Kano ta ‘rugurguje’ karin Sarakuna 4 da Ganduje ya kirkira

0

Wata babbar Kotun tarayya dake da zama a jihar Kano, ta ruguza karin Sarakuna 4 da gwamnatin jihar Kano karkashin jagoranci Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta kirkira.

Mai shari’a Usman Na Abba, wanda ya yanke hukunci yace Majalissar jihar Kano bata bi ka’ida ba wajen aminta da kirkirar sarakunan guda hudu.

Tin dai a watan Mayun daya gabata ne dai gwamnan Kano, Dr Ganduje, ya sanya hannu akan karin masarautun Bichi, Karaye, Rano da Gaya.

An dai zargin gwamnatin ta Kano da kokarin rage darajar Sarkin Kano Muhammadu SUnusi II, bayan da tsagin gwamnatin jihar suka zargeshi da goyon bayan dan takarar gwamnan Kano a karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020