Dan wasan kasar Masar, Mohammed Salah ya samu nasarar zama gwarzon dan kwallon Africa a karo na biyu.
Dan wasan mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar Ingila, ya zama gwarzon dan wasan ne a karo na biyu bayan gagarumar rawar da yake takawa a kungiyarshi da ma kasar shi ta Masar.
Dan wasan ya kara da abokin buga kwallonsa a kungiyar ta Liverpool dan kasar Senegal, Sadio Mane tare da takwaranshi na kungiyar Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, na kasar Gabon.
Dan wasan ya wakilci kasar Masar a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka gudanar a kasar Rasha a shekarar 2018.
Ya ci kwallaye 24 a wasannin da ya buga a kakar wasanni ta 2018.