Kwabid19: Lafiyar Mamman Daura lau, ziyara ya tafi Burtaniya – inji Iyalansa

Karatun minti 1

Bayan wasu jaridun kasar nan sun bayyana cewa dan uwan shugaban kasa, Muhammadu Buhari wato Mallam Mammam Daura an dauke shi cikin gaggawa zuwa kasar Burtaniya domin rashin lafiyarsa ta hasala, iyalan Daura sun karyata hakan.

Rahoton da DABO FM ta samu ya bayyana cewa ko kadan Malam Mamman ba alamun cutar Koronabairas bane suka saka ya fita daga kasar ba, Daura dai wasu nayi masa kallon daya daga cikin wanda suke da juya gwamnatin shugaba Buhari.

A ranar Laraba jaridun kasar nan suka bayyana an fitar dashi kasar waje domin wahalar numfashi da kuma wasu alamu da suka yi kama da cutar Korona, inda majiya daga iyalansa tuni suka karyata hakan.

Sai dai kuma abinda ya kuma jawo cece kuce bai wuce wasu na ganin tafiyar ta Malam Mamman Daura taci karo da dokar hana shiga da ficen zuwa kasashen waje da gwamnati tasa sanadiyar karr yaduwar cutar Korona, wanda sai 29 ga Ogusta za’a sahale dokar. Kamar yadda Vanguard ta fitar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog