Labarai Taskar Matasa

Mun kafa Gidauniyar Hadiyatul Khair domin kawo karshen talauci – Mufidah Fari

Shugabar gudanarwar Gidauniyar Hadeeyatul Khair, ta bayyana cewa sun kafa kungiyar ne a wani mataki na taimakawa al’umma tare da kawo karshen talauci a yankin Arewacin Najeriya.

DABO FM ta tattara cewar Gidauniyar Hadeeyatu Khair, gidauniyace dake da mazauni a jihar Kano, inda take taimakawa mutane musamman mata wadanda suke cikin tsananin bukata.

A wata sanarwar da shugabar gidauniyar, Dr Fatima Mufida Ibrahim Fari ta aikewa DABO FM ta ce kungiyar tana baiwa mata jari domin dogaro da kawunansu hadi da taimakawa yara wajen sama musu guraben karatu a matakin Firamare da Sakandire.

“Mun kafa gidauniyar don kawo karshen talauci ga Al’umma tare da taimaka wa mabukata, bayarwa mata jarin dogaro da kai tare da daukar nauyin yara don saka su a makarantun addini da zamani.”

A kwanakin baya tin watan Yulin 2019, DABO FM ta rawaito yadda gidauniyar ta kai tallafin kayayyakin abinci zuwa gidajen marayu da gidajen yari a jihar Kano.

Haka zalika shugabar tace sun bude shafin koyar da sana’o’i da wasu darussan tafiyar da rayuwa a shafin yanar gizo-gizo.

Daga karshe tayi kira ga masu son bayar da gudunmawa ko zama daga cikinsu lo kuma yin rijistar fara karatun yanar gizon ya tuntubesu a lambobin kasa.

UA-131299779-2