Home LabaraiGwamnatin Tarayya ta gargadi shuwagabanni akan furta zantuka ‘yadda suka ga dama’

Gwamnatin Tarayya ta gargadi shuwagabanni akan furta zantuka ‘yadda suka ga dama’

by Dabo Online
0 comments

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, ta gargadi shuwagabanni da jami’iyyu da su kiyaye harsunansu wajen yin magana.

Gwamnatin ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da kakakin fadar gwamnatin Mallam Garba Shehu, ya fitar yayin cikar shekaru 50 da yin yakin basasan Najeriya.

Garba Shehu yace abin mamaki ne cewar har yanzu wasu sun ki koyar darussa akan yakin da ya janyo asarar rayuka dayawa ta hanyar yin kalamai da har yau zasu iya kawo rarrabuwar kai tsakanin ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa; lokacin yayi da yakamata a manta da abinda ya faru, a kuma dauki darasi tare da kokarta saka soyayyar kasa da fatan cigaban kasar a nan gaba.

“Yau da muke girmama shekaru 50 da kawo karshen yakin basasa, muna tunawa da girmama wadanda suka rasa rayukansu na kowanne bangare. Bazamu taba mantawa da abinda ya faru ba, haka zalika bazai sake faruwa ba.

“Yakin basasar da yakamata a zama gargadi bisa hatsarin dake tattara da nuna kabilancin yanki, kabilancin kabila da amfani da siyasa wajen ginuwar kai ba al’umma ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00