Home LabaraiMutane sun fara kaura daga gidajensu bayan kasar Chadi ta janye Sojojinta dake Borno

Mutane sun fara kaura daga gidajensu bayan kasar Chadi ta janye Sojojinta dake Borno

by Dabo Online
0 comments

Bayan rahotannin janyewar dakarun Sojin Chadi da tafiyar Sojin Najeriya daga garin Gajiganna na jihar Borno, al’ummar garin sun fara hijirar barin garin domin gujewa harin mayakan Boko Haram.

Tin dai da yammacin yau Asabar, jaridar AFP ta rawaito cewar kasar Chadi ta janye dakarunta guda 1200 daga Najeriya wanda a yanzu haka babu ko Sojan kasar guda a a Najeriya.

Majiyoyin AFP sun tabbatar da yacce ‘yan garin Gajiganna a adadin da yafi daruruwa suka rika ficewa daga garin domin tsoron wani harin mayakan Boko Haram a nan gaba.

Majiyar tace: “Suna tafiya, yawanci mutanen garin Gajiganna sun tsere zuwa Maiduguri saboda tsoron harin ‘yan ta’adda. Sunyi kaura ne bisa dalilin tafiyar dakarun Najeriya dake aiki tare da dakarun kasar Chadi da suka koma kasarsu.”

Daga cikin wanda suka kauracewa garin nasu zuwa Maiduguri, ya bayyanawa AFP cewar; “Na baro Gajiganna zuwa Maiduguri a ranar Laraba lokacin da na fuskanci Sojojin Najeriya sun bar sansaninsu lokaci kadan bayan janyewar dakarun kasar Chadi.”

Ya bayyanawa AFP cewar; “Dani da kimanin mutane 300 mun bar garin bayan da muka ga janyewar dakarun Sojin. Muna ji ne kamar an barmu sakaka ba a tsare ba.”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00