Mutum-mutumi ya karbe aikin ‘Yan Sanda a kasar Sin

Mutum-mutumi na farko ya fara gudanar da ayyukan ‘yan Sanda a kasar Sin(China)Kamar yadda aka tsara shi a kan hakan.

Shi dai wannan Mutum-mutumi yana dauke da Kamarorin tsaro a jikinsa,da kuma Tayu na mota, da karfin Giga Biyar na tsarin Takanologi(5G)

An dai saki wannan Mutum-mutumi ne a birnin Shanghai na kasar ta Sin.

Wannan Mutum-mutumi duk aikin da yayi yana tura sakonninsa ne kai tsaye zuwa ga ofishin ‘Yan Sanda da alhakin kula da shi ya rataya a wuyan su.

Ko sai Yaushe irin wannan ci gaban zai zo Najeriya?

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

Masu Alaƙa  Hotuna: Wutar Lantarki a Birtaniya ta kara daukewa bayan gyara a shekaru 16
%d bloggers like this: