Labarai

Dambarwar Gandujiyya da Kwankwasiyya: An kama Naziru Sarkin Waka

Yanzunnan mun samu rahoto cewa jami’an tsaro sun kama mawaki Naziru Ahmad, Sarkin wakar Sarkin Kano wanda aka fi sani da Sarkin Waka.

A wani rahoto da Nasiru Salisu Zango, ma’aikacin gidan Rediyo Freedom dake jihar Kano ya fitar, ya tabbatar da kamun mawakin a yau Laraba.

“Yanzun nan akaje gidan Nazir Sarkin wakar Sarkin Kano, aka kama shi.”

“Anje neman beli, ance sai dai gobe a dawo.”

DABO FM ta bincika cewa hukumar tace finai finai ta jihar Kano ce tayi umarnin kama mawakin bisa zarginshi da keta wata dokar hukumar.

Sai dai ga dukkanin mai bibiyar al’amuran siyasar jihar Kano, za’a iya alakanta kamun mawakin da rashin nuna goyon bayanshi ga tafiyar gwamnatin jihar Kano.

Duba da shigar jarumai da mawakan fina-finan Hausa, hakan ya baiwa gwamnatoci musamman ta jihar Kano damar cin zarafin jarumai ko mawaka da suka barranta daga goton bayan gwamnatin jihar.

Makwanni da suka gabata, aka kama mai bada umarni a masana’antar Kannywood, Sunusi Oscar, akan laifin da bashi da hurumi a ciki.

Sabon salon dambarwar tsagin siyasar Kano dai ya baiwa mai gwamnati damar cin karenshi ba babbaka wajen yin amfani da jami’an tsaro su kame wanda yake hamayya da ita.

Masu Alaka

Da Dumi Dumi: Rarara ya saki sabuwar waka tun gabanin hukuncin kotun koli

Muhammad Isma’il Makama

Yanzu-yanzu: Sarkin Karaye ya nada Kwankwaso Makaman Karaye kuma hakimi mai nada sarki

Muhammad Isma’il Makama

Aisha Kaita: Shekaran jiya tana PDP, jiya ta shiga APC, yau tayi tsalle ta koma PDP

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2