(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Na fahimci Saudiyya bata son baiwa mata yanci da auren jinsi – Dalilin Nicki na soke chasu a Jedda

Karatun minti 1

Fitacciyar mawakiyar Hip-Hopa kasar Amurka, Nicki Minaj, ta soke bikin chasun da zata halarta a birnin Jedda dake kasar Saudiyya.

Nicki Minaj ta soke zuwa chasu ne bisa dalilinta na goyon bayan ‘yancin mata dana fadar albarkacin baki da goyon bayan ‘yan luwadi da ‘yan madugo.

Kasashen yamma sun dade suna zargin kasar Saudiyya ta tauye hakkokin dan adam musamman na mata.

Kafin mawakiyar ta soke zuwa chasu, an shirya gudanar da chasun ne a birnin Jedda a ranar 18 ga watan Julin 2019.

“Bayan nayi duban tsanaki, na yanke shawara kin zuwa wasan da zanyi a wajen Bikin Chasun Duniya a birnin Jeddah.”

Duk da buri na bai wuce in samarwa da masoyana a Saudiyya Arabia farinciki ba, sai dai na fuskanci irin yanayin da mutanen kasar suke ciki.

“Yana da matukar amfani in bayyana goyon bayana ga ‘yancin mata da yancin damar zama dan luwadi ko dan madugo tare da ‘yancin fadar albarkacin baki.”

Tin satin daya gabata ne dai hukumar kare hakkin bil’adama ta aike wa Nicki Minaj sakon jan hankali tare da shawararta ta akan kar taje wajen chasu bisa dalilin tauye hakkin dan adam da kasar Saudiyya takeyi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog