Buhari ya fitar da N62.7b domin gyara titin da ya tashi daga Kano, Dawakin Tofa, Gwarzo zuwa Dayi

Karatun minti 1

Kwamitin zartarwa na ƙasa ya bada umarnin fitar da naira biliyan 62.7 domin yin aikin da ya tashi daga Kano zuwa Dawakin Tofa ya dangana da Gwarzo har zuwa Dayin jihar Katsina.

Da yake shaida wa Dabo FM, wakilinmu ya bayyana sanarwar ta fito daga bakin Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ranar Laraba a Abuja lokacin da ake zaman majalisar zartarwa ta ƙasa.

Babatunde Fashola ya kuma kara da cewa aikin zai dauki tsawon watannin 24 kafin a kammala shi.

Da yake karin bayani ministan yaɗa labarai, Lai Mohamed ya bayyana kwamitin ya kuma fitar da N470,263,037 domin gyaran filin tashin jiragen sama na Murtula Muhammad da ke Ikko.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog