Najeriya ta samu nasara a wasanni 5 daga cikin 17 data buga da kasar Tunisiya

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles ta samu nasara a wasanni 5 kacal daga cikin jimillar wasanni 17 da kasashen biyu suka taba bugawa.

DABO FM ta binciko cewa tarihi ya cewa, kasar Tunusiya ce tafi yin galaba akan Najeriya.

Tunisiya ta samu nasara a wasanni 6 yayin da Najeriya ta samu nasara a wasanni 5 wanda hakan ya nuna sunyi canjaras 5.

DABO FM dai ta kara bincikowa cewa kasashen sun fara karawa a shekarar 1961 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekarar 1962. Najeriya ce ta samu nasara da kwallo 2 da 1.

Sun kuma buga wasa na karshe a shekarar 2009 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya na 2010 wanda wasan ya kowacce kasa tana da kwallo 2.

Masu Alaƙa  Kasar Madagascar tana kan chasa Najeriya a gasar AFCON

A ranar Laraba ne dai ake sa ran kasashen biyu zasu sake haduwa a wasan neman na 3 a gasar cin kofin nahiyar Afrika na shekarar 2019 da ake yin a kasar Misra.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.