Labarai

Buhari ya amince da ginin sabuwar kwalejin ilimi a jihar Bauchi

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kirkirr sabuwar kwalejin ilimi a jihar Bauchi dake arewacin Najeriya.

DABO FM ta tattara cewar shugaban ya amince da ginin sabbin kwalejin ilimi guda 6 wadanda za a ayi a kowanne sashi na Najeriya.

Hakan na kunshe a cikin wata takarda mai lamba SAF.36/S.623/I/36 da DABO FM ta shaida wadda ma’aikatar ilimi ta aikewa gwamnan jihar, Bala Muhammad a ranar 16 ga watan Afrilun 2020.

“Ina sanar da kai cewar shugaba Buhari ya amince da kafa sabbin kwalejin ilimi a dukkanin yankunan Najeriya guda 6 domin tunkarar karancin makarantun da ake fama dasu musamman a jihohin da babu irin wadannan makarantu.”

“A sakamakon haka, shugaban ya amince da a gina sabuwar kwalejin a garin Jama’are dake karamar hukumar Jama’are.

Takardar mai dauke da sa hannun sakataren ma’akatar, Arc. Sonny S.T Echono tace za ta aike da ma’aikatanta da hukumar dake ba da izinin kafa kwaleji domin su yi duba domin ganin inda ya dace ayi kwalejin.

Har yanzu dai Najeriya na fama da rashin isassun makarantu neman ilimi.

A wani labarin kuma zaku ji cewar mutane 4641 ne suka kamu da cutar Kwabid19 a fadin Najeriya zuwa yanzu da safiyar ranar Talata, 19 ga watan Ramadana.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi miliyan 20 a zango na biyu – Minista

Dabo Online

Gwamnati ta shirya tsaf domin fara karbar haraji daga hannun mutane milayan 45 -Shugaban Haraji

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin tarayya zata fara rabawa ‘yan Zamfara N5000 a kowanne wata – CCT

Dabo Online

Babu wani shugaba kuma ‘Janar’ dan damukuradiyya kamar Buhari -Yahaya Bello

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin tarayya za ta cigaba da yin ayyukan raya kasa da kudin ‘Yan Fansho – Aliero

Dangalan Muhammad Aliyu

Babu wani ci gaba da Buhari ya samu a yaki da Boko Haram -Kungiyar Tarayyar Turai

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2