Labarai

Osinbajo ya bambanta Sanusi da sauran sarakuna, ya kira su ‘Dagatai da Shuwagabannin Al’ada’

Mataimakin Shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki mafi daraja inda ya kira sauran Sarakuna da Dagatai da Shugabannin al’ada.

Rahoton Dabo FM ya bayyana Osinbajo ya fadi hakan ne a sanyin safiyar Talata kan shafin sa na Twitter bayan ya bar garin Kano yayin wata ziyarar bude aiki daya je jihar Kano.

Farfesa Yemi yace “Naje na hadu da Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kuma mun danyi mu’amala da sauran Dagatai da shugabannin gargajiya, inda na ziyarci babban gidan tarihi na kasa baki daya.”

Wannan bayani na Osinbajo dai makwannin kadan da suka wuce fadar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari tayi irin makamancin sa inda ita ma ta bayyana Sarki Sanusi a matsayin Sarkin Kano daya tilo.

Inda masu nazari ke ganin jawabin fadar Shugaban kasar shi ya jawo kara takun saka tsakanin Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarki Sanusi a yan kwanakin nan, wanda har Gwamnatin ta Kano ta bawa Sarki kwana 2 rak ya karbin karin sarakuna ko ta tsige shi.

Karin Labarai

Masu Alaka

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Bamu da wani babban buri illa sake gina ‘Yankin Arewa maso Gabas – Osinbajo

Dabo Online
UA-131299779-2