Labarai

Masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a Zaria da Kubau da kuma Kauru sun koka

Masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a kananan hukumomin Zaria da Kauru da kuma Kubau a jihar kaduna, sun koka game da lalacewar azuzuwa da rashin karishe aiki daga ‘yan kwangila da kuma rashin tsaro a wasu makarantu yankunan nasu.

Sun bayyana haka ne da suke gabatar da mabanbanta ra’ayoyin su a taron karawa juna sani na kwana daya, da cibiyar tabbatar da ‘yancin Dan Adam da kuma inganta inganta ilimin jama’a wato CHRCED a takaice tare da hadin gwiwan gidauniyar MacArthur suka shirya a Zaria.

Taron da ya mayar da hankali akan ayyukan da hukumar kula da ilimi ta jihar kaduna wato SUBEB ke aiwatarwa a kananan hukumomin Zaria da Kauru da kuma karamar hukumar Kubau.

Mafi akasarin mahalarta taron, daga karamar hukumar Kubau sun koka kan yadda wasu ‘yan kwangila suka yi watsi da ayyukan da aka basu musamman na ginawa tare da gyara dakunan karatu makarantun gwamnati a yankin.

Kuma sun bayyana yadda wasu makarantu, kamar GGSS Anchau da CPS Anchau da kuma wasu makarantu ke zama cikin halin ni’yasu lokacin damina, saboda lalacewar rufin dakunan karatun yara.

Yayin da kuma suka yabawa hukumar ta SUBEB, saboda ayyukan da suka gudanar a wasu sassan karamar hukumar.

A karamar hukumar Kauru kuwa, mahalarta taron sun bayyana matsalar tsaro a matsayin abun da ke ci masu tuwo a kwarya, kuma suka roki gwamnati ta taimaka wurin killace makarantu da suke a bude domin samun tsaro mai inganci.

Yayin da a Karamar hukumar Zaria, masu ruwa da tsakin suka koka kan yadda ake samun karancin azuzuwa da rashin kayan koyarwa na zamani a wasu daga cikin makarantu.
Yayin da wasu suka jaddada rokon samun wadataccen ruwa da karin dakunan karatu a yankunan su.

Tun farko da yake jawabin maraba, shugaban kungiyar ta CHRCED Kwamared Ibrahim Zikirullah, ya ce manufar shirya irin wannan ganawar, shi ne domin al’umma su samu tsari mai kyau a bangaren koyo da koyarwa, kuma ana yi ne ta yadda za’a gina rayuwar yara masu tasowa ta hanya mai kyau.

A cewar shi, suna fatan a karshen taron a samu tsari mai kyau da kuma fadarkar da gwamnati hakkin da ya rataya a kanta, domin inganta harkar samar da ilimi a fadin jihar kaduna.

UA-131299779-2