Labarai

Rikicin masu Sarauta Biyu a Masarautar Zazzau ya kai ga Kotu

Kotun Majestare da ke ‘yan Azara Tudun Wada Zaria, karkashin jagorancin Malam Muhammad Sada Abdulkadir, ta fara sauraren karar da Garkuwan Makarantar Zazzau, Alhaji Shamsudeen Aliyu Mai Yasin, ya shigar, yana tuhumar Alhaji Yusuf Jafaru, Sarkin Tudun Wadan Zazzau, da kuma sauran mukarraban sa mutum uku, bisa laifin bata suna da cin mutumci da kuma tsoratarwa, kuma bisa wannan, ya naimi kotun ta bi masa hakkin sa tare da hukumta wadanda ake zargin.

A zaman da kotun ta yi a Litini 31 ga watan Satumbar 2019, karkashin jagorancin mai Shari’a Muhammad Sada Abdulkadir, An kira wanda ake karar mutum Hudu, sai dai mutum Uku ne kawai suka samu halartan kotun, banda shi wanda ake karar, Sarkin Tudun Wadan Zazzau Alhaji Yusuf Jafaru.

Nan ne lauyan mai karar Alhaji Shamsudeen Aliyu Mai Yasin, Barista S M Aliyu, Ya tashi ya gabatar da kansa ga kotu kuma ya fadi dalilin shigar da karar tasu.

Daga bisani sai Alkali Muhammad Sada Abdulkadir, ya naimi sanin ko ina cikon Mutum na Hudu da ake kara Alhaji Yusuf Jafaru, Wanda Kuma da hakan lauyan da ke kare wandanda ake karar Barista Abubakar Sulaiman, ya gayawa kotu cewa, shi cikon na Hudun bai samu takardan sammacin sa ba har zuwa lokacin fara Shari’ar saboda hujjar cewa, ya yi tafiya.

Daga bisani kotun ta sanya ranar Litinin 7 ga watan Oktoba domin ci gaba da shari’ar.

UA-131299779-2