Taskar Matasa

Neman Ilimin Addini da na Boko wajibi ne – Amina Salanke

Zariya, Nigeria

An bayyana naiman Ilimi, a matsayin wani abu da ya zama wajibi kuma dole a halin da ake ciki a yau, domin shi ne kadai madogara da mutum zai tsira da mutuncin sa da kuma samun rayuwa mai kyau.

Shugaban Kungiyar Mata Musulmi ta FOMWAN ta Karamar Hukumar Zariya, Hajiya Amina Abdulkadir Salanke, ta bayyana hakan, da take zantawa da manema labarai, a gefen taron yayen salibai na Makarantar Safinatul Khairiyya, da ke Anguwar Nagoyi a Karamar Hukumar Zariya.

Hajiya Amina Salanke, ta ce, naiman ilimi wani bangare ne na cika umarnin Manzon tsira Annabi Muhammad S.A.W, da ya bukaci a naimi Ilimi ko da a birnin Sin ne.

Ta kara da cewa, naiman Ilimi ba batun rashi ne ko akwai na kudi ba, domin yau a ko’ina akwai wurare da aka bude makarantu da majalisan naiman Ilimi a karkara da birane.

Ta bayyana sadaukarwa, a matsayin wani janibi da ke zama kan gaba wurin habaka naiman Ilimi a yau.

Ta shawarci iyaye, su dage kuma su yi iya kokarin su, wurin samar da Ilimi ga yaran su.

“Ilimi ba’a gado, baiwa ce da Allah ya ke ba wasu kebantattun mutanen da ya so, Kudi ana gado, amma Ilimi ba’a gado”, Inji Hajiya Amina Abdulkadir.

Ta yaba ma Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dr Shehu Idris, saboda kiran da yake a ko da yaushe, domin ganin an baiwa yara masu tasowa ilimin da ya dace, kuma ta shawarci gwamnati, ta hanyar fitowa da matakai saukakawa, domin rage matsalolin da ake fuskanta a fagen ilimi a yau.

Kuma ta yaba ma Marigayi Alhaji Muntaka Comassie, saboda gudunmuwar da ya jima yana bayarwa, na gina makarantu da masallatai, ciki kuwa har da makarantar ta Safinatul Khairiyya, domin bunkasa rayuwar masu tasowa.

A jawabin sa, Shugaban Makarantar, Malam Umar Idris, ya ce, wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da yayen daliban, kuma ya gode ma iyayen yaran makarantar saboda gudunmuwar da suke ba su a koda yaushe, sannan ya yi fatan samun ninkin hakan a gaba.

Masu Alaka

Ginin babban dakin karatun Abuja zai lakume Naira biliyan 50 – Ministan Ilimi

Dabo Online

El-Rufa’i zai kaddamar da shirin bada ilimi kyauta a Kaduna

Muhammad Isma’il Makama

Zamu fara kama iyayen da basa saka ‘yayansu a makaranta – Malam Adamu

Dangalan Muhammad Aliyu

Za a fara yiwa ‘yan Najeriya da sukayi a Digiri a kasashen ketare binciken kwakwaf

Rilwanu A. Shehu

Dole ku sanya yaranku a makarantun gwamnati – El-Rufai ga jami’an gwamnatin Kaduna

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2