Umar Aliyu Fagge
Ra'ayoyi

Romon Dimokradiyya: Kura da shan bugu Kato da kwace kudi, Daga Umar Aliyu Fagge

Kura da shan bugu kato da kwace kudi!

Wannan salon maganar shi ne mafi dacewa da halin da siyasar wannan zamani ta tsinci kanta a ciki. Romon demokradiyya (Dividends of democracy) wani kabakin alheri ne da wasu daga cikin yan siyasa masu rike da madafun iko suke gwangwaje alu’mmar da suke mulka ko wakilta a matakai daban-daban, ana yin amfani da wannan tsarin a siyasa ne gurin ganin cewa mutane da dama sunci ribar demokradiyya ba wai sai kawai wanda suke da shaidar karatu na gaba da sakandiri ne suke da damar ribatar siyasa ba.

Mafi akasarin lokaci yan siyasa na yin amfani da wannan salon gurin tattara mutanen da ya kamata ace sun samu wata dama a siyasa amma basu samu ba, saboda wani dalili wanda ya kore musu wannan damar misali:- Malaman Islamiya masu bawa yara tarbiya da ma’aikatan wucin gadi da sauran mutanen gari wanda ba zasu iya shiga hayaniyar siyasa ba amma suna goyon bayan wannan tafiyar.

Amma abin takaici yanzu abubuwan duk sun lalace mutanen da ya kamata ace sunfi gajiyar wannan tsarin na romon demokradiyya basu ne suke samu ba, saboda su basa daya daga cikin biyun mutanen da zasu zagi shugaba ko su dauki maganar wane su kai wa wancan. Mutanen da suka sarayar da mutuncinsu a lokuta da dama don samun wannan romon demokradiyyar sune dai a kan gaba a duk lokacin da wani dan siyasa zai bada irin wannan gudunmawar.

Kullum ana fifita masu yin banbadanci akan mutanen da suka tsare mutuncinsu kuma suke amfanar da alumma ta fuskoki daban-daban.

Yanzu so ake su wadannan mutanen kirkin su juye izuwa irin nau’in wadancan mutanen?

Ya bayyana karara cewa yan siyasar wannan zamani sun fi ganin daraja da kimar wadancan mutanen da suke aikata banbadanci ko munafurcin akan wadanda suke tarbiyantarwa tare da taimakon alu’mma ta fuskoki daban-daban, bugu da kari akwai yan jam’iyyar da ya kamata ace sun kasance a cikin wannan tsarin amma an dakile su saboda basa daga cikin masu aikata wancan mummunan aiki da suna biyyaya ko goyon baya ga wani dan siyasar!
Gyara kayanka dai……….

Rattabawa 
Umar Aliyu Musa
[email protected]
10/1/2020
06:05pm

Karin Labarai

Masu Alaka

Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani

Ko mutanen Arewa zasu so Kwankwaso irin soyayyar da Buhari ya samu?

Dangalan Muhammad Aliyu

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso a fafutukar darewa kujerar Lamba 1?

Dabo Online

Alakar dan Majalissar tarayya na Fagge da Al’ummar da yake wakilta, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online
UA-131299779-2