WIN-WIN: Siyasar zaro idanuwa da jagoranta Mu’azu Magaji

dakikun karantawa
Engr Mu'azu - Salon Hoton WIN-WIN

A cikin makon da muke bankwana da shi, ga ma’abota amfani da Facebook za su ga yadda mutane ke wallafa hotunan dauki da kanka, su zaro idanu tare da rataya wani dogon yadi a wuya. Hakan ba komai bane face alamar tafiyar WIN-WIN.

Tafiyar WIN-WIN, tafiya ce ne da jagoranta, Engr Mu’azu Magaji, tsohon Kwamishinan ayyuka na jihar Kano ya ce ana yi ne ‘don sauya salon siyasar jihar Kano wajen bai wa matasa damar shiga cikin siyasa’ tare da kawo karshen mulkin kama-kama da a cewarsa aka dade anayi tsakanin manyan gidajen siyasar Kano.

Sai dai duk da manufar da jagoran yake ikirarin ya sanyawa tsarin, wasu daga cikin al’ummar Kano musamman sanannu a shafukan sada zumunta sun mai da abin wasa tare da ‘bin yarima a sha kida’ wajen wallafa hotunan zare idanuwan da nufin suna goyon baya, har ta kai ga maimakon sunan tsarin na ‘WIN-WIN Canji, suna yin shaguben cewa WI-WI Caji.

Alamu sun nuna cewa wasu daga matasan Kano sun gamsu da sabon tsarin WIN-WIN. A makon da muke bankwana da shi, wasu matasa suka gayyaci Engr M’uazu Magaji taron mai taken ‘Makomar Matasa’ wanda aka gudanar da wani wajen taro dake Titin Magaji Rumfa a birnin Kano.

Kazalika wasu matasa da ke sana’ar Kafinta sun hada wa jagoran WIN-WIN doguwar kujera da ‘babu mai tsawonta a duk fadin masarautun arewacin Najeriya.’

Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya
Engr.-Muazu-Magaji-Dan-Sarauniya

Kalmar  WIN-WIN nasara ce ko faduwa ga Engr Mu’azu Magaji?

Fara wa da duban asalin yadda kalmar ta hadu,  a iya cewa ita ce sanadiyyar tsige Engr Mu’azu daga kan kujerarsa ta Kwamishinan Ayyuka na jihar Kano bayan ya yi amfani da kalmar a sakon da ya wallafa lokacin da Abba Kyari ya rasu. Ranar 18 ga Afrilun 2020, DABO FM ta rawaici wasu kalamai da Mu’azu ya yi wadanda aka kalla a matsayin murya da mutuwar Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan shugaba Buhari da cutar Koronabairas ta hallaka.

Mu hadu a muƙala ta gaba.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog