Labarai

Sarkin Musulmi da Sheikh Sharif Saleh sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya

Sarkin Musulman Najeriya, Sultan Abubakar Saad, Sheikh Sharif Saleh Ibrahim da shugaba Muhammad Buhari sun samu shiga sahun sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya na shekarar 2020.

Lambar yabon da Cibiyar binciken Musulunci ta Royal Islamic Strategic Studies Center ta kasar Jordan, ta saba fitarwa duk shekara.

DABO FM ta tattara cewa Sarkin Musulmai da shugaba Muhammadu Buhari sun shiga cikin Musulmai 50 masu fada aji-a fadin duniya a bayan Sarkin kasar Morocco, Muhammad na 6 da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamid Al-Thani da sauransu.

Shugaba Buhari ya samu zama Musulmi na 17 mai fada aji-afadin duniya, Sarkin Musulmai ya shiga jerin da lamba ta 20.

Haka zalika Sheikh Ibrahim Saleh na jihar Borno a Najeriya ya shiga cikin jerin Malaman Muslunci na duniya guda 40.

DABO FM ta tattara cewar cibiyar ta sanya Sheikh Ibrahim Saleh a matsayin malamin Musulunci na 30 a fadin duniya, wanda yazo a bayan malamai irinsu Sheikh Dr Yusuf Al-Qaradawi na Qatar da sauransu. Ya kuma zo a gaban malamai irinsu Dr Zakir Naik na kasar Indiya da Sheikh Abdulrahman Al-Sudais na kasar Saudiyya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu-Yanzu: Jihohin Kano da Kaduna sun lashe Musabakar karatun Al-Kur’ani ta Najeriya

Dabo Online

Sarkin Musulmi, Sheikh Ibrahim Saleh da Buhari sun shiga sahun Musulmai 500 masu fada-a-ji a duniya

Dabo Online
UA-131299779-2