Labarai Siyasa

Operation tsamar Nama: Shugaban PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ya koma APC

Engr Rabiu Sulaiman Bichi, shugaban PDP na jihar Kano kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya ya koma jami’iyyar APC.

Hakan na zuwa ne kwanaki daya bayan hukuncin kotun koli ta tabbatar da Dr Ganduje a matsayin gwamnan jihar Kano.

Ana sa ran a ranar Laraba, Rabiu Sulaiman Bichi zai bayyana komawarshi jami\iyyar ta APC tare da wasu magoya bayanshi/.

DAILY NIGERIAN ta tattara cewar majiyar jami’iyyar APC ce ta bayyana haka inda ta kuma tace ficewar Bichi daga jami’iyyar ba tada alaka da rashin nasarar da jami’iyyar PDP tayi a kotun Koli.

“Barin jami’iyyar tashi bashi da alaka da hukuncin koli. Yayi haka ne domin rajin kanshi ba dan komai ba.” – A cewar wani makusancin Rabiu Bichi.

“Rabiu ya zama wata saniyar ware a tafiyar Kwankwasiyya wanda har takai ba’a sashi a cikin jigogin tafiyar masu zartarwa. Ana masa kallon mai yin zagon kasa.”

Rabiu Bichi shine tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano a lokacin mulkin tsohon gwamna Engr Rabiu Kwankwaso 2011-2015, haka zalika shekarar farko ta mulkin Dr Ganduje (2015-2016).

Tsohon shugaban ma’aikayar tsara birane ta jihar Kano, KNUPDA wanda daga bisani ya zama kwamishina duk dai a mulkin Engr Kwankwaso daga 1999 zuwa 2003.

UA-131299779-2