Labarai

Sarkin Musulmi ya amince a gabatar da Sallar Idi a Masallatan Juma’a

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Abubakar Sa’ad III, ya yi ga Musulmi su gabatar da Sallar Idi a masallatan Juma’a na garuruwansu.

DABO FM tattara cewar kiran ya shafi iya garuruwan da gwamnatocinsu suka amince su gabatar da Sallar Idi.

Hakan na kunshe a ciki wata sanarwa da kwamitin dake baiwa Sarkin Musulmi shawarwari kan harkokin addinai ya fitar a ranar Alhamis.

Wannan na zuwa ne bayan da Jama’atul Nasril Islama da Sarkin Musulmi ke jagoranta ta dakatar da gabatar da Sallar Idi a kan iyakokin garuruwa, wajen gari da guraren da baza a samu kulawar jami’an bada kariyar lafiya ba.

Karin Labarai

UA-131299779-2