Labarai

Dalilan da suka sa aka yankewa Yunusa ‘Yalo’ hukuncin shekara 26

Biyo bayan hukuncin da aka yi wa matashin nan dan jihar Kano, Yunusa Dahiru ‘Yellow, akan zargin sace wata budurwa daga jihar Bayelsa a 2015.

DABO FM ta tattara cewar tin a shekarar 2015, aka zargi matashi Yunusa Yellow ya sace wata yarinya mai suna Ese Oruru daga jihar Bayelsa zuwa Kano tare da zargin yi mata fyade wanda ta kai ga ta dauki ciki.

A yau Alhamis, 21 ga watan Mayun 2020, wata Kotun Tarayya dake da zamanta a garin Yenagua, ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 26.

Lauyan da yake kare Yunusa Yellow, Barista Kayode Olaosebikan, ya zayyana wasu daga cikin dalilan da suka kai ga yanke hukuncin da ya kai shekaru 26.

Lauyan yace; Mun samu kalubale a yayin gudanar da shari’ar tin farko. Akwai wasu shaidu guda 6, biyu daga cikinsu mazauna jihar Bayelsa, 4 daga cikinsu suna jihar Kano.”

“Sai munyi kokarin samun dukkaninsu, amma bamu samesu ba. Idan aka duba wannan hukuncin, za a ga cewar kotu ta bamu lokaci mai tsawo domin gabatar da hujjojinmu.”

Lauyan ya kara da cewa bisa dalilin uzururruka da ya baiwa kotu, ta dage zaman shari’ar so da yawa domin su gabatar da shaidunsu amma basu samu zo gaban kotu ba.

“Kotu ta bamu da dayawa, ta dage zaman shari’ar sau hudu zuwa biyar domin mu samu damar gabatar da shaidunmu a gabanta amma basa zuwa, saboda haka babu abinda zamu iya yi.”

Baya ga haka kuma, cikin wata tattaunawa da lauyan nan mai kare hakkin bil’adama, Barista Audu Bulama Bukarti ya yi tare da Barista Abba Hikima a shafin Facebook, sun bayyana wasu daga dalilan da zasu iya zama wadanda suka kawo wa shari’ar matsala.

Sai dai a cewar Audu Bulama, ya samu dalilan ne daga wata lauya da yace tayi tsayin daka wajen kare Yunusa Yalo a gaban Kotu.

Bulama yace lauyar ta fada masa cewar dawowar matashin daga jihar Bayelsa zuwa jihar Kano tare da kin komawarshi a lokutan da kotu take bukatar ya bayyana a gabanta ya bayar da matsalar da kotu ta soke belin Yalo da ta bayar tin da fari.

Karin Labarai

UA-131299779-2