Ƙasar Amurka ta ce tana neman malaman yarukan Hausa da Yarabanci domin koyarwa a makarantun ƙasar.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ne ya sanar da neman malaman a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin yanar gizon ofishin.
DABO FM ta tattara cewar masuza buƙatar aikin za sun iya nema daga ranar 1 ga Fabarairu har zuwa 1 ga watan Yuni, shekarar 2021.
Sanarwar ta ce malaman za su koyar da yarukan Hausa da Yarabanci murka d tare da al’adunsu.
Kazalika, ta ce aikin da za su yi a kasar zai basu damar cigaban da karatu a wasu fannoni daban daban na ilimai.
Sharuɗa da yadda za a iya neman aikin koyar da Hausa a Amurka.
Karanta a nan: https://bit.ly/2YCR5cv