Shattiman Dutse ya cika shekaru 60 a kan karagar Mulki

Karatun minti 1

A yau Juma’a 4 ga watan Okotoba, na shekarar 2019, mai girma Shattiman Dutse Hakimin Gundumar Yayari dake karamar Hukumar Buji cikin jihar Jigawa yake cika shekaru 60 da rike da sarauta a hannunsa.

A wata takarda da mai girma Madakin Kano ya saka wa hannun ranar 04/10/1959, ta tabbatar da ba shi sarautar Digachin Yayari.

Takardar mai lamba Kamar haka:
STM/5/393, tana bayyana wa Hakimin Birnin-kudu na wancan lokacin cewa, mai Martaba sarkin Kano Sunusi na masarautar Kano ya Nada Garba dan Muhammad Digachin garin Yayari, bayan rasuwar Marigayi Muhammad Tsohon Digachin.

A shekarar 1997 kuma mai Martaba sarkin Dutse, Alh. Dr. Nuhu Muhammad Sunusi ya Daga darajarsa zuwa Hakimi, a masarautar Dutse ta jihar Jigawa.

Baya ga haka an ba shi mukamin Shatima a wancan lokaci, bayan gunduna da yake da ita ta Hakimci.

Alh. Garba Muhd Yayari, yayi shekaru 38 yana Digachi, sannan yayi shekaru 22 yana Hakimimci.

Har kawo Yanzu haka, yana nan cikin koshin lafiya, yana gudanar da harkokin sarauta na yau da kullum.

Shattiman Dutse Alh. Garba Muhd Yayari, yayi zaman Hakimci a wadannan Gundumomi Kamar haka:

  1. Gundumar Miga
  2. Gundumar Fagam
  3. Gundumar Buji
  4. Gundumar Yayari

Wadda yanzu haka yake a Gundumar Yayari, tun Daga shekarar 2013 zuwa yau.

Muna addu’ar Allah ya kara wa Yayan mu Hakimi Lafiya da tsawon rai

Karin Labarai

Sabbi daga Blog