Ma’aikatan da Gwamnatin jihar Katsina ta dauka aiki don rage musu radadin talauci, sun yi barazanar tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.
Hakan na zuwa ne bayan korafin da ma’aikatan sukayi akan cewa ba’a biyansu albashi.
Ma’aikatan sun bayyana tafiyarsu yajin aikin ne a wata takarda da Sakataren gamayyar ma’aikatan, Aliyu BK, ya fitar a ranar 29 ga watan Oktoba.
Gwamnatin jihar Katsina ce ta bullo da S-Power, kwarar N-power ta Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Sun bayyana shiga yajin aikin ne daga ranar 7 ga watan Satumba zuwa lokacin da gwamnatin zata waiwayesu ta biyasu albashi duk tsawon lokacin da za’a dauka.
Zuwa yanzu da muke hada wannan rahotan, mun kira sakataren kungiyar ma’aikatan domin karin haske, inda ya bayyana mana yana Masallaci.
