Sheikh Al-Zakzaky zai tafi kasar Indiya bayan shafe kwanaki 1337 a tsare

Jagoran tafiyar masu bin mazahabar Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya kama hanyarshi ta zuwa kasar Indiya domin neman magani.

DABO FM ta binciko cewa; An dai kama shugaban kungiyar IMN da gwamnati Najeriya ta haramta, Sheikh Al-Zakzaky tin a watan 14 ga watan Disambar 2015.

Hakan ya saka malamin ya zama yayi kwanaki 1337 a hannun jami’an tsaron Najeriya bayan wata ‘yar takadamma da ta barke tsakanin ‘ya yan kungiyar da jami’an Sojojin Najeriya.

A lokacin da Al-Zakzaky yake hannun jami’an tsaro, tsohon Ministan yada labaran Najeriya, Lai Muhammad, ya bayyana cewa; Gwamnati tana kashe Naira miliyan 3 wajen ciyar da Al-Zakzaky.

Idan kuna biye da al’amuran Najeriya, a ranar 5 ga watan Agusta na 2019, kotu ta bada belin Al-Zakzaky domin zuwa kasar Indiya bayan da lauyanshi, Femi Falana SAN, ya gabatar da kudirinshi na zuwa neman zaman lafiya a kasar ta Indiya.

Tini dai Al-Zakzaky ya bar kasar Najeriya zuwa kasar Indiya a ranar Litinin da misalin karfe 6 na Yamma jirgi kirar Emirates mai mataki na farko ya bar Najeriya zuwa kasar ta Indiya.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.