Hakiman Kano sun bijirewa uwarnin Ganduje, sunyi mubayi’a ga Sarki Sunusi

Hakimai a jihar Kano sun bijirewa umarnin gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje.

Ganduje ya baiwa dukkanin Hakiman Kano umarni da “Kowanne Hakimi yayi hawan bikin Sallah a Masarautarshi.”

Sanarwar da babban mataimakin gwamnan kan fannin Labarai, Abba Anwar ya sanar a ranar Idin Babbar Sallah ta 2019 biyo bayan umarnin da Masarautar Kano ta baiwa Hakimai da suzo gaban Sarki domin suyi hawan Sallah.

Sashin Hausa na Legit.ng ya tattaro cewa; Hakimai 11 ne suka bijirewa umarnin Ganduje tare da yin hawan Daushe tare da tawagar Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

“Daga cikin Hakiman da suka kauracewa umarnin Ganduje tare da yin biyayya ga sarkin Kano, Sanusi II, sune; Madakin Kano; Yusuf Nabahani (hakimin Dawakin Tofa), Dan Amar; Aliyu Harazimi Umar (hakimin karamar hukumar Doguwa), Muhammad Aliyu (hakimin Garko), Makama; Sarki Ibrahim (hakimin Wudil), sarkin fulani; Ja’idinawa Buhari Muhammad (hakimin karamar hukumar Garin Malam, da Barde; Idris Bayero (hakimin karamar hukumar Bichi).

Ragowar sune; Sarkin Bai; Adnan Mukhtar (hakimin karamar hukumar Danbatta), Yarima Lamido Abubakar (hakimin karamar hukumar Takai), Dan Isa; Kabiru Hashim (hakimin warawa), Dan Madami; Hamza Bayero (hakimin karamar hukumar Kiru) da Sarkin Dawaki Mai Tuta; Bello Abubakar (hakimin karamar hukumar Gabasawa).

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.