Labarai

Yajin aiki babu gudu ba ja da ba – ASUU

Kungiyar ASUU ta bayyana yakin aikin da ga shiga a matsayin na babu gudu babu ja da baya indai har basu cimma matsaya tsakaninta da gwamnatin Najeriya ba.

Kungiyar ta sake jaddada matsayarta ta a yayin wani taro da shugabanni kungiyar suka gudanar a garin Yola dake jihar Adamawa.

Kungiyar ta kira yakin aiki da takeyi a matsayin wanda zsi kawo sauyi a jami’o’in Najeriya.

Tin dai a makon da ya gabata ne dai kungiyar ta shiga yajin aiki a wani matsayi irin na kalubalantar gwamnatin Tarayya kan batun dorasu a sabon tsarin IPPIS.

‘’Dole ke sa wa mukan je yajin aiki, dubi yadda gwamnati kan yi shakulatin bangaro game da yarjejeniyar da aka yi a baya. Ai muna wannan fafutukar ne domin kawo gyara,” a cewar Farfesa Augustine A. Ndaghu, wanda ya halarci taron.

Masu Alaka

Taraba: Kungiyar ASUU ta kara tafiya yajin aikin sai baba ta gani

Dabo Online

Kungiyar ASUU ta tsage gida 2

Dabo Online
UA-131299779-2