Shugaba Buhari ya gaza
Ra'ayoyi

Shugaba Buhari wasa yake da hankulan talakawa – Shamsu Kura

‘Shugaban Talakawa’, Shamsuddin Kura, daga cikin sojojin baka a jihar Kano, ya bayyana shugaba Buhari a matsayin wanda yake wasa da hankulan talkawana Najeriya.

Da yake bayyana haka a shirin Kowanne Gauta da gidan Rediyon Freedom a jihar Kano yake yi, ‘shugaban talakawa’ yace fadin shugaba Buhari na cewa zaben da aka gudanar a shekarar 2019 sahihi ne, ba wani abu bane illa wasa da hankalin talakawa.

Matashin ya kara da cewa “tin daga lokacin da shugaba Buhari yace babu wanda zai lashe zaben shugaban kasa sai shi” yakamata a gane cewar maganar da yayi na cewa zaiyi gaskiya ta rushe.

DABO FM ta tatara cewar ranar 23 ga watan Fabarairun 2019, a lokacin da shugaba Buhari yake amsa tambayar, “Ko zai taya wanda ya lashe zabe murna? Shugaban yace shine zai lashe zaben.

Daga karshe ya kuma bayyana takaici kan yacce shugaba Buhari bai dauki mataki kan rikici-rikicen da suka faru a lokacin zaben jihar Kogi wanda har yayi sanadiyyar rasuwar wata shugabar mata.

Karin Labarai

UA-131299779-2