Katsina: Gidauniyar Kwankwasiyya za ta kafa asusun fitar da dalibai karatu kasashen Duniya

Karatun minti 1

Tini shirye shirye yayi nisa na kafa asusun kai ‘ya’yan talakawa a jihar Katsina wanda Gidauniyar Kwankwasiyya ta dauki gabaran yi bayan ta samu nasarar kai fiye da daliban jihar Kano 200 karatu kasashen duniya.

Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa shugaban hukumar ‘Pleasant Library da Book Club (PLBC)’, Injiniya Muttqha Rabe Darma, ne ya bayyana haka.

A cikin wata tattaunawa da Darma yayi ya fada cewa kungiyar sa ta gayyaci tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso domin ya kaddamar wa jihar Katsinan dikko irin asusun tallafi da ya kaddamar a Kano.

Yace “Naji Sanata Kwankwaso ya nuna aniyar sa ta kafa wannan asusu a jihar Katsina da sauran jihohi a Najeriya, wannan shine babban dalilin daya sa nayi saurin tintibar sa akan batun.”

“Irin wannan tinani shi muke bukata a siyasa.” Darma ya bayyana cewa shi kansa ya bada gudunmawa irin wadda yake so ya kara assasawa a jihar Katsina. Kamar yadda jiridar KatsinaPost ta fitar.

Ya bayyana ya daukin nauyin dalibai fiye da 140 da kudin fansho da giratuti bayan da ya gama aikin shugabancin hukumar PLBC.

Asusun dai zai dauki nauyin ‘ya’yan talakawan jihar ne domin samun ilimin zamani a fadin Duniya, a cewar shugaban.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog