Labarai

Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ya mika ragamar shugabancin Jami’ar

Shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Ibrahim Garba, ya mika ragamar shugabancin jami’ar ga mataimakinsa na sashen karantarwar jami’ar, Farfesa Danladi Amodu-Ameh a matsayin shugaba mai rikon kwarya.

Farfesa Ibrahim Garba, ya mika ragamar gudanarwar ne a ranar Juma’a yayin taron hukumar gudanarwar ta jami’ar.

Shugaban, wanda wa’adinsa zai kare a ranar 30 watan Afrilu 2020, ya yi kira ga mutanen jami’ar da su bai wa sabon shugaban rikon kwarya cikakken goyon baya wajen gudanar da ayyukansa.

A kwanakin baya ne aka ruwaito cewa, rikici ya barke tsakanin shugaban da kuma babbar majalisar gudanarwar jami’ar lokacin da suka bukaci ya ajiye mukaminsa domin daukan hutun shi na barin aiki ranar 1 ga watan Mayu 2020, bayan wata wasika da magatakardar jami’ar Malam A. A. Kundila ya rattabawa hannu.

A wani labarin makamancin wannan kuma, Jami’ar Ahmadu Bellon ta yi bukin rantsar da sabbin dalibai sama da dubu 10 da suka samu guraben karo karatu a bangarori daban-daban na Jami’ar.
Da yake jawabin wurin rantsar da sabbin daliban, shugaban Jami’ar mai barin gado farfesa Ibrahim Garba, ya shawarce su da su guje ma shiga kungiyoyin asiri da aikata badala da kuma satar jarabawa yayin zaman su a Jami’ar.

Kuma ya hore su, su kasance jakadu na gari ga Jami’ar a duk inda suka tsinci kan su.

UA-131299779-2