Labarai Siyasa

Har yanzu ni dan jam’iyyar PDP ne -Kwamishinan Ganduje

Kwamishinan ruwa na jihar Kano, Sadiq Wali ya bayyana cewa shifa har yanzu yana cikin jam’iyyar sa ta PDP duk da kuwa yana rike da mukami mai gwabi a gwamnatin jam’iyyar APC karkashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Majiyar Dabo FM daga jaridar KanoFocus ta rawaito cewa Kwamishinan ruwan yaje ya karbi katin jam’iyyar PDP a matsayin sabuwar shahadar sa tare da mahaifin sa Ambasada Aminu Wali, Bello Hayatu Gwarzo da sauran tawagarsu.

Wannan ya biyo bayan zargin tade jam’iyyar da uwar jam’iyya ta kasa take ganin sunyi a jihar Kano.

Idan za’a iya tinawa dai jam’iyyar ta PDP ta dare gida biyu tun lokacin da daya daga cikin iyayen wannan jam’iyya wato Amb. Aminu Wali yayi kokarin sanya dansa a matsayin dan takarar gwamna.

A bangaren tsohon gwamna Kwankwaso ma dai ya fitar da yaron sa wanda ta karfi dai ya zama dantakar jam’iyyar bada son wancan tsagin ba.

Bayan nasarar Ganduje akan Abba Kabir, tsagin Wali karkashin jagorancin Yahaya Bagobiri sun kaiwa gwamnan jam’iyyar adawa ta APC ziyarar taya murna tare da mubaya’a.

Wanda a daidai wannan lokaci ne majiyar mu ta jiyo Bagobiri na fadin su sukayi umarni da tsagin su na PDP ya dangwalawa dan takarar jamiyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje.

UA-131299779-2