Taskar Malamai

#JusticeForKano9: So muke ayi mana adalci akan Yaranmu da aka canza wa Addini – Dr Rijiyar Lemo

Sheikh Muhammad Umar Rijiyar Lemo, malamin addinin Musulunci a Najeriya, yayi kira da hukumomi da suyi adalci akan Yaran jihar Kano wadanda aka mayar dasu Kiristoci.

Makonnin da suka gabata ne dai hukumar ‘yan Sanda reshen jihar Kano, suka kwato wasu Yara yan jihar guda 9 da aka sace aka kuma chanza musu addini a garin Onitsha dake jihar Anambra.

A wani zaman karatu da Malamin ya gabatar a ranar Litinin, 21 ga watan Oktobar 2019, Malamin yayi tsokaci tare da yin Allah wadai da al’amarin daya faru.

DABO FM ta tattara cewa; Sheikh Rijiyar Lemo, yayi kira da hukumomin gwamnati da su dauki matakin daya dace wajen ganin an hukunta mutanen da suka aikata ta’asar satar yaran.

“Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da manyan kasa, su fito suyi Allah wadai da wannan abu sa’annan su nuna lallai-lallai za’a hukunta wadanda aka samu dumu-dumu da wannan laifuka, ayi hukuncin da hankalin kowa zai kwanta.”

Sheikh Rijiyar Lemo, ya yaba wa rundunar ‘yan sandan jihar Kano karkashin jagoranci Kwamishina, Ahmad Iliyasu, bisa hubbasar da sukayi wajen lalubo wadannan yaran.

Ya kuma yayi kira ga al’ummar Musulmi da suyi hakuri, kar su nuna fushi ta hanyar daukar doka a hannu.

“Baza mu zuga wani muce yayi wani abu ba, bamu yadda wani yace zai dauki doka a hannunshi ba, a bar wadanda al’amarin yake hannunsu. Tinda har sun dauko wannan aiki, zamuyi musu fatan alheri kuma muyi musu addu’a ta Allah Ya tsare su.”

Daga karshe yayi kira ga iyaye Musulmi da su kula da ‘ya ‘yansu kamar yacce addinin Musulunci ya tanada.

“Muma a wurinmu, muyi duk abinda zamuyi wajen tsare ‘ya’yanmu da wajen kare zamantakewar mu kuma yana da kyau mu rike duk wani abu da zai tabbatar mana da zaman lafiya.”

Masu Alaka

Mu guji zagi da cin mutuncin Malaman Addini da Shuwagabanni, yin hakan kamar zubar da jini ne – Dr Rijiyar Lemo

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2