Labarai

Jami’ar Maiduguri ta kara kudin Makaranta zuwa akalla N200,000

An wayi gari da kara wa Daliban Jami’ar Maiduguri kudin Makaranta “da ya wuce hankali” – a cewar Daliban.

DABO FM ta tattaro cewa a ranar Talata, hukumar gudanarwar jami’ar ta fidda jadawalin sabon kudaden da daliban makarantar zasu biya a zangon da za’a shiga.

A zangon daya gabata, sabon Dalibi yana biyan N30,000-40,000 ne. Amma a sabon jadawalin Yanzu haka, akwai Daliban da za su biya Naira 100,000 da wani abu,yayin da wasu kuma za su biya Naira 200,000 da wani abu.

Kudin Makaranta yayi tashin gwauran zabi, wanda ya linka kudin da daliban suka biya a zangon daya gabata da kashi 50-70. Sabbin dalibai na wasu bangarorin karatu zasu biya kimanin N100,000, N144,000 da kuma N200,000. – Kamar yacce majiyar ta bayyana mana.

DABO FM ta tattabar da cewa; Tsoffin Daliban dake karantar fannin Likitanci (MBBS) ‘yan shekara ta 3,4,5, da 6, zasu biya jumillar N165,000 a zangon da za’a shiga hadi da dakunan kwana, N103,000 banda kudin dakunan kwana.

Daliban MBBS, ‘yan shekarar farko da shekara ta 2, zasu biya N119,000, babu kudin dakunan kwana. N174,000 hadi da wajen kudin dakunan kwana.

A zangon daya gabata dai sabbin dalibai sukan biya N33,000 inda tsofaffin dalibai suke biyan N18,000.

Tini dai daliban Makarantar suka fara nuna damuwarsu game da karin kudaden wanda yasa wasu daga ciki suke neman a sanar dasu “Ko jami’ar da koma da kudi?”

Haka zalika, kungiyar daliban jihar Borno ta hannun sakatarenta, Suleiman Mailafiya, ta bayyana kokenta bisa ga karin kudin makarantar.

“Kashi 70 na daliban wannan Jami’ar dukkanin su ‘yan jihar Borno ne, wadanda rikicin rashin zaman lafiya yasa Iyayensu suke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira.

“Muna tunanin bisa wannan dalili hukumar jami’ar nan zata rage kudin makarantar da kaso 50, sai kuma muji kawai kudin yayi tashin gwauron zabi.”

“Bisa haka yasa, wannan kungiyar take neman karin bayani daga hukumar makaranta akan karin kudaden da tayi.

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben2019: Abubuwan fashewa sun tashi a Maiduguri

Dabo Online

An kai hari Jami’ar Maiduguri

Rilwanu A. Shehu

Da ‘Dumi ‘Dumi: Boko Haram sun kai hari Chibok

Muhammad Isma’il Makama

An zargi ‘yan Boko Haram da hannu a hari yayin Sallar ‘Tahajjud’ a Maiduguri

Dabo Online
UA-131299779-2