Jaipur, India (DABO FM) – A ranar Asabar, dakarun Sojin Najeriya sun afka wa jami’an yaki da cutar Kwabid-19 da gwamnatin jihar Borno ta kafa ciki har da kwamishina a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewar tini dai daya daga cikin ‘yan kwamitin ya riga mu gidan gaskiya in da guda hudu kuma suka samu munanan raunuka.
Al’amarin ya faru a garin Auno ne a dai dai lokacin da jami’an kwamitin suka tare wasu motocin mutane da na sojoji domin tabbatar da dokar da gwamnatin jihar ta saka na haramta shige da fice cikin jihar, kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.
Daga cikin membobin kwamitin, Kwamishinan shari’a na jihar, Kakashehu Lawal da Salisu Kawaya Buram, wani jami’in lafiya, sun bayyana cewar sojojin sun ritsa su da bindigogi duk da sun basu shaida da kuma yi musu bayanin aikin da suke yi.
Kwamishinan ya zargi sojojin da yin amfani da karfin tuwo wajen shiga jihar, ya ce sun kuma bude wa mutane hanyar shiga jihar ba tare da la’akari da wadanda dokar hana zirga-zirga ta haramtawa shiga jihar ba.
Ya ce sojojin da suka yi ikirarin zuwa tunkarar mayakan Boko Haram a garin Gubio sun zo a cikin motoci guda 3 kirar Hilux, suka kuma tamfatsi motar da aka durke domin hana shiga cikin jihar.
Ya kara da cewa dukkanin mutane da suke cikin motar sun ji munanan raunuka.
Kwamishinan ya ce duk da hargitsi da aka samu, ya nemi jami’an ‘yan sandan da suke tare da su zauna cikin nutsuwa ba tare da shiga rigimar ba.
“A matsayinmu na ‘yan Najeriya, mun san fatan gwamnatin shugaba Buhari da shugaban Sojin Najeriya bai wuce kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu ba.”
“Don haka baza mu bar wani kaso na sojoji su haifar da duk wani nau’in cin zarafi na mutanen da suke a bakin aikinsu ba.”
Shi ma jami’in lafiyar, Salisu Kawaya Buram ya ce sojojin sun yi ta barin mutanen da ba a yi bincike a kansu ba suna shigar jihar.
A nashi bangaren, kwamandan sashi na 7 na rundunar sojin, Sunday Igbinomwanhia, ya bai wa kwamitin hakuri ya kuma alkauranta bincike akan lamarin.
