Home Taskar Malamai‘Ba Allah wadai za ka yi akan kisa a Arewa ba, idan baza ka iya daukar mataki ba, ka sauka’

‘Ba Allah wadai za ka yi akan kisa a Arewa ba, idan baza ka iya daukar mataki ba, ka sauka’

by Dabo Online
0 comments
Sheikh Nuru Khalid_Buhari

Jaipur, India (DABO FM) – Sheikh Nuru Khalid, fitaccen malamin adddinin Islama ya nuna takaicin kalaman shugaba Muhammadu Buhari da ya ce ya saba yi duk lokacin da aka kashe mutane a Arewa.

Malamin ya ce in banda a yankin Arewa, babu wani yanki a Najeriya da za a yi kisan kiyashi ko ka kuwa na kaji ba mutane ba kuma ace sama da shekaru ba a dauki mataki ba.

Ya kuma nuna takaicin rashin bai a bangaren tsaron al’ummar arewa muhimmanci.

“Idan da gaske ne don kar mu mutu aka rufe mana masallatai da kasuwanni an kuma karya mana tattalin arziki to ya ake kashe mu kuma ake shiru? Don me ake kashemu kuma ba a yi komai ba?

A cikin jawabin da malamin ya yi wanda DABO FM ta kalla, malamin ya kira shugaba Buhari da ya gyara ko kuma ya sauka in da a bangare guda kuma ya yi togaciya ga mutanen da suke nuna bangarenci wajen zaben shugaba ba tare da bin nagarta ba.

“Maganinku ne ma kuma ai kune da matsala. Ranar zabe sai ku haukace kuna cewa “ai jihadi ne. Wallahi Kiristoci za su kwace Najeriya.”

To shike nan ba su kwace Najeriyaba. An barta a hannun wanda zai zauna ana kashe ku iya abinda za a yi wai sai ace “Shugaban kasa ya yi Allah wadai”. Wane irin Allah wadai? An zabe shi ne domin yayi Allah wadai? An zabe shi ne domin ya dau mataki. In ba zai iya daukar mataki ba to ya sauka.”

A wani labarin kuma za kuji cewar ‘yan binduga sun sake kai hari kauyen Mazoji na jihar Katsina tare da hallaka shugaban kauyen a yau Asabar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00